Gwamnan Ebonyi ya dakatar da basaraken gargajiya saboda kashe-kashen da ake yi a yankin sa

0
90

Gwamna David Umahi na Ebonyi ya dakatar da basaraken al’ummar Isinkwo da ke karamar hukumar Onicha, Mista Josephat Ikengwu bisa ci gaba da kashe-kashen da ake yi a yankinsa.

Sakataren gwamnatin jihar (SSG), Dr Kenneth Ugbala, ya bayyana a ranar Lahadi a Abakaliki cewa dakatarwar da aka yi wa basaraken ya fara aiki nan take.

Ugbala ya lura cewa Ikengwu ya gaza a cikin alhakin da ya rataya a wuyansa na dakatar da kashe-kashen da ake yi a cikin al’umma.

“Saboda haka, zai mayar da dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsa, ciki har da motarsa, ga hukumar ta SSG a ko kafin rufe aiki a ranar Litinin, 17 ga Oktoba, 2022,” in ji Ugbala. (NAN)