Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a yankin Tigray na kasar Habasha, tare da kira ga bangarorin da ke rikici da juna tsawon shekaru biyu da su shiga tattaunawar sulhu kai tsaye.
Shugaban gudanarwar kungiyar ta tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat ne ya yi wannan kira da kakkausar murya, inda ya bukaci tsagaita wutan ba tare da wani sharadi ba tare da dawo da ayyukan jin kai a yankin.
Faki Mahamat ya ce yana bibiyar rahotannin da ake samu na tashe-tashen hankula a yankin na Tigray, kuma yace abin tada hankali ne da matukar damuwa.
Mayakan Tigray sun yaba
Tuni Mayakan Tigray ta bakin kakakin su Getachew Reda, sunyi maraba da wannan kira “bisa la’akari da mummunan rikicin jin kai da ke faruwa a yankin nasu sakamakon abin da ya danganta da hare-haren da sojojin Eritrea da kawayenta na Habasha kaiwa kansu.”
To sai bangarorin gwamnati da sojin Habasha sunki cewa komai kan wannan batu, haka zalika Ministan yada labaran Eritiriya Yemane Gebremeskel bai amsa bukatar jin ta bakinsa ba.
Tun 2022 rikici ya barke
Gwamnatin Habasha da kawayenta da suka hada da sojojin Eritriya na ci gaba da fafatawa da dakarun Tigray tun daga karshen shekarar 2020. Rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban fararen hula tare da raba miliyoyi da gidajensu.
Bangarorin biyu dai sun zargi juna da haifar da rikicin.