Ba ni na ba da umarnin tsare El-Rufai a Anambra ba – Peter Obi

0
82

Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi, ya musanta zargin bai wa jami’an tsaro umarnin tsare Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yayin zaben Gwamnan Jihar Anambra a 2013.

Obi ya musanta zargin ne bayan El-Rufai ya ce dan takarar ya ba da umarnin a tsare shi a 2013, a lokacin da El-Rufai ke a wajen taron siyasa da aka shirya a ranar Litinin.

El-Rufai ya ce ya je Anambra a wacan lokaci a matsayin jami’in Jam’iyyar APC don sanya ido a kan zaben gwamnan jihar.

Amma ya ce jami’an tsaro sun tsare shi a otel din da ya sauka bisa umarnin Obi wanda shi ne Gwamnan Jihar Anambra a lokacin.

Sai dai, Obi ya ce babu hannunsa a umarnin da aka bayar don tsare El-Rufai.

Ya ce, “Yanzu da na shigo, wani ya shaida mini cewa dan uwa, Gwamnan Kaduna ya ce da ya zo jihata na sa an tsare shi. Bari in fada muku, yana da kyau a wayar da kan jama’a idan irin wannan ya faru.”

Obi ya ce, baki daya shekara takwas da ya yi yana gwamna, watannin ukun farko ne kadai ya yi ba tare da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar daga Arewa ba.

Ya ce, lokacin da El-Rufai ke zargin an ba da umarnin tsare shi din, lokacin zabe ne, kuma Kwamishin ’Yan Sanda da Sufeta-Janar na ’Yan Sanda da mataimakinsa da aka turo aikin zaben baki dayansu ’yan Arewa ne.

Don haka ya ce a matsayinsa na gwamna karkashin Jam’iyyar APGA ba shi da karfin da zai ba da umarnin tsare wani, hasali ma ya ce shi kansa an tsare shi a yankin karamar hukumarsa.