Mun cika wa ‘yan Najeriya alkawarin da muka yi musu a shekara 7 – Buhari

0
80

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da auna kwazon ma’aikatun gwamnatinsa na kasarshe, inda ya bayyana cewa sun kaddamar da manyan ayyuka a sassa daban-daban na kasar nan domin cika wa ‘yan Nijeriya alkawarin da suka yi musu.

Da yake magana kan sake shirya kwatanta kwazon da gwamnatinsa ta samu, shugaban kasa ya lissafo wasu daga cikin nasarorin da ya samu a bangaren gona da tattalin arziki da lafiya da yakar cin hanci da rashawa da dai sauransu.

Shugaban kasa ya shaida wa mahalarta taron ciki har da tsohon shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta cewa sama da hanyoyi da suka kai kimanin kimomita 3,800 ya gina a fadin kasar nan, yayin da aka saya wa rundunar sojojin saman Nijeriya jiragen yaki har guda 38 domin fatattakar masu ‘yan ta’adda.

Ya kara da cewa ‘yan Nijeriya miliyan 38.7 sun samu nasarar yin allurer rigakafin Korona, wanda ya sa aka samu kashi 35 na yawan ‘yan Nijeriya da suka yi rigakafin cutar.

A bangren kayayyakin more rayuwa kuwa, shugaban kasan ya ce gwamnatinsa ta samar da muhimman ayyukan ci gaban kasa da farfado da tattalin arziki wanda ta bar kyakkyawar tarihi.

Ya ce, “Wasu daga cikin nasarorin da muka samu sun hada da kammala hanyar Itakpe zuwa Ajaokuta ta nufi Warri mai nisan kimomita 326 da titin dogo da ke tsakanin Lagas zuwa Ibadan mai nisan sama da kimomita 156.5 da kuma kammala babban aikin tashar jirgin ruwa da ke Apapa a Jihar Legas.

“A bangren ayyukan hanya kuwa, wannan gwamnatin ta shiffida hanyoyi da suka kai kimomita 408 da gyara hanyoyin da suka kai kilomita 15,961 a dukkan sassa daban-daban da ke kasar nan.

“Manyan ayyukan hanyoyi da aka gina sun hada da gadar Neja mai tsawon kilomita 1.9 da ta hade jihohin Anambra da Delta, sannan an gyara hanyar Legas zuwa Shagamu ta nufi Ibadan mai hannu biyu da kuma ta Abuja zuwa Kaduna ta nufi Zariya har ta kai Kano da dai sauransu.

A cewasa, gwamnatin tarayya a karkashinsa ta yi namijin kokari wajen samar da ayyukan ci gaban kasa a shekarun bakwan da ta shafe a kan karagar mulki. Buhari ya ce gwamnatin tarayya ta gina hanyoyin tarayya har guda 21 wanda suka kasance jimillar nisansu ya kai kimomita 1,804.6.

Shugaban kasa ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta yi kokari wajen bunkasa harkokin sufuri a filayen jiragen saman da ke fadin Nijeriya. Ya kara da cewa gwamnatinsa ta farfado da tattalin arziki wanda a baya ya samu koma-baya a wata ukun shekarar 2020.

A bangaren harkokin man fetur kuwa, shugaban kasa ya tunatar da cewa a ranar 16 ga watan Agustan 2021 ya rattaba hannu kan kudirin dokar man fetur wanda ya zama doka tare da samar da sauyi wajen kulawa da kamfanin mai na kasa. Ya ce dokar ya samar da kyakkyawan tsari da ya bunkasa kamfanin mai na kasa wajen kulawa da harkokin man Nijeriya.

A fannin karfafa tsaron kasa kuwa, shugaban kasa ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi kokarin samar da makamai na zamani da wasu muhimman kayayyakin sojoji tare da ba su horo wajen tunkarar ‘yan ta’adda. Ya ce gwamnatinsa ta samu nasarar kara yawan ‘yansanda ta hanyar daukar sababbin jami’ai har guda 20,000 a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021.

Bangaren yaki da cin hanci da rashawa kuwa, Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bankadowa tare da gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

Haka kuma a bangaren shirye-shiryen bunkasa zamantakewa kuwa, shugaban kasa ya ce, ana ciyar da daliban makaranta guda 9,990,862 a karkashin wannan shiri tare da daukar masu dafa aminci aiki har guda 128,531.