Ambaliya ta kashe mutum 195 a Nijar

0
73

Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 195 tare da shafar rayuwar wasu 322,000, a Jamhuriyar Nijar.

Hukumomin kasar sun ce 59 daga cikin mamatan ruwa ne ya ci su, 136 kuma faduwar gini a kansu ne ya kashe su, sannan wasu sun samu raunuka.

Hukumar Kare Al’umma ta Jamhuriyyar Nijar ta bayyana cewa ambaliyar da aka samu a daminar bana na cikin mafiya muni a tarihin kasar.

A farkon watan Oktoba da muke ciki hukumar ta sanar cewa ambaliya a daminar bana ta yi ajalin mutum 192 tare da shafar rayuwar wasu dubu 263 a kasar.

Ambaliya ta kuma lalata gidaje 3000 a ajujuwan makarantu 83 da cibiyoyin lafiya 6 da ma’ajiyar hatsi
 235.
Yankunan da ambaliyar ta fi yin barna su ne Maradi, Zinder, Dosso da kuma Tahoua.
A 2021, mutum 70 sun rasu sakamakon ambaliya da ta taba mutum 200,000.
A 2020 kuma mutum 73 ne suka rasu.