Sojoji sun ceto karin ’yan matan Chibok

0
79

Sojojin Najeriya sun ceto karin dalibai biyu da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su shekara takwas da suka gabata a Makarantar Sakandaren Kwana ta ’Yan Mata da ke Chibok a Jihar Borno.

Da yake gabatar da daliban da aka  ceto bayan sun shekara takwas a hannun ’yan Boko Haram, Babban Kwamandan Rundun ta 7 da ke Maiduguri, Manjo-Janar Shuaibu Waidi, ya ce za a mika su ga Gwamnatin jihar Borno.

Manjo Janar Shuaibu ya ce, Yana Pogu mai lamba 19 a jerin ’Yan Matan Chibok da aka sace, sojoji sun ceto ta ne tun a ranar 29 ga watan Satumba tare da yara hudu, a kauyen Mairari, a Karamar Hukumar Bama, a yayin wani sintiri na share fage.

“Hakazalika, a ranar 2 ga Oktoba, aka kara ceto Rejoice Sanki, wacce ke lamba 70 a jerin ’Yan Matan Chibok, sojoji sun ceto ta tare da ’ya’yanta biyu a yankin Kawuri,” in ji Janar Waidi.

Ya ce yanzu haka ana duba lafiyar daliban da aka ceto tare da ’ya’yansu domin a mika su ga gwamnatin Borno.

“A halin yanzu za sojojinmu sun ceto ’Yan Matan Chibok 13 a cikin watanni biyar da suka gabata.

“Ya zuwa yanzu, daga cikin ’Yan Matan Chibok 276 da ’yan ta’addan suka sace a shekarar 2014, saura 96 a hannun ’yan ta’addan Boko Haram.

AMINIYA