Faransa ta fara gudanar da bincike a kan amfani da jirage marasa matuka a rikicin Ukraine

0
75

Kasashen Faransa da Birtaniya da Jamus sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta gudanar da bincike kan jiragen Iran marasa matuka da kasashen Yamma suka ce Rasha na amfani da shi wajen yakin Ukraine.

Duk da ci gaba da tabarbarewar rikicin, Faransa na dagewa kan mahimmancin bude layukan sadarwa da shugaban Rasha Vladimir Putin ya katse.

“Za mu yi maraba da binciken da tawagar sakatariyar MDD da ke da alhakin sa ido kan aiwatar da shirin na UNSCR 2231,” in ji jakadun MDD na kasashen uku a wata wasika a ranar Juma’a.

Kudirin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231 ya amince da yarjejeniyar kasa da kasa da ta tanadi sassauta takunkumin da aka kakaba mata domin dakile shirin nukiliyar Iran — yarjejeniyar da shugaban Amurka na lokacin Donald Trump ya soke.

A cikin wasikar tasu wacce aka aike wa kwamitin sulhu da Sakatare-Janar Antonio Guterres, jakadun sun ce “za su tashi tsaye don tallafawa ayyukan sakatariyar wajen gudanar da bincikenta na fasaha.”

Sun kara da cewa sun damu matuka da batun jigilar jiragen yaki marasa matuka daga Iran zuwa Rasha wanda ya saba wa kudurin.

“Wadannan jiragen UAV Rasha ne ke amfani da su a yakin da take yi da Ukraine wajen kai hare-hare kan ababen more rayuwa da biranen Ukraine, lamarin da ya kai ga mutuwar fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba.

Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya Nicolas de Riviere ya yi kira ga Iran da ta gaggauta dakatar da duk wani nau’in goyon bayan da Rasha ke yi wa Ukraine.

Kasashen yammacin duniya sun zargi Iran da samar da jiragen da Moscow ke amfani da su wajen kai hare-hare a Ukraine, kuma fadar White House ta fada jiya alhamis cewa jami’an Iran suna cikin kasa a Crimea suna taimakawa sojojin Rasha wajen kai hare-hare.

Sai dai wakilin Rasha na Majalisar Dinkin Duniya, Vassily Nebenzia, ya kira tuhumar da “wani labari na karya game da kayayyakin da ake zargin Rasha…Mun yi watsi da duk wani yunkuri na shigar da sakatariyar MDD cikin wannan kazamin aiki.”

Ita ma Iran ta yi watsi da kakkausar murya kan zargin da ake yi mata na jirage marasa matuka a Majalisar Dinkin Duniya a farkon makon nan.