Shugaban China ya kafa tarihin samun wa’adi na uku kan karaga

0
182

Shugaban China Xi Jinping ya samu wa’adi na uku a wannan Lahadin domin ci gaba da jagorancin kasar , yayin da ya yi wa wasu makusantansa na jam’iyyar Kwaminisanci karin girma, lamarin da ke tabbatar da matsayinsa na shugaba mafi karfin fada-a-ji da aka gani a kasar tun bayan Mao Zedong.

Kwamitin zartaswar jam’iyyar ta zabi Xi a matsayin babban sakataren jam’iyyar don yin jagorancin shekaru biyar.

Shugaba Xi mai shekaru 69 na da tabbacin ci gaba da mulkar kasar a karo na uku, inda za a ayyana tazarcensa a hukumance a yayin babban taron gwamnatin kasar da za a gudanar a cikin watan Maris mai zuwa.

Sake zaben sa na zuwa bayan babban taron da wakilai dubu 2 da 300 daga jam’iyyarsa suka gudanar a cikin mako guda, inda suka amince da salon shugabancin Xi, sannan suka amince a yi garanbawul na gaggawa wanda ya tilasta wa masu takara da shi janyewa.

Kazalika babban taron na jam’iyyar Kwaminisanci wanda shi ne karo na 20, ya kuma nada sabbin mambobin kwamitin zartaswa da ya kunshi jiga-jigan ‘yan siyasa 200, wadanda suka taru a wannan Lahadi domin zaben Xi da kuma wasu kusoshin jam’iyyarsu.

Tun dai lokacin da ya zama shugaban China shekaru 10 da suka shude, Xi ya samu nasarar tattara karfin mulkin kasar wuri guda wanda ba a taba ganin irinsa ba tun lokacin Mao.

A shekarar 2018 ne, shugaba Xi ya rushe tsarin wa’adi biyu kacal ga shugaban kasa, inda ya yi wa kansa sharen-fagen yin tazarce kan karagar mulki har sai-baba-ta-gani.

Shugaban dai ya jagoranci kasar har ta kai matsayin ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, yayin da ya fadada karfin sojin kasar da kuma karfafa barazanarta a duniya, lamarin da ya janyo mata adawa daga Amurka.

Koda yake shugaban na China zai fuskanci manyan kalubale a sabon wa’adinsa na shekaru biyar da suka hada da bunkasa tattalin arzikin kasar da ke fama da bashi, sai kuma zazzafar adawa daga Amurka.

RFI