Hukumomin Gwamnatin Tarayya 20 za su kashe biliyan N29.32 wajan sayen kayan makwalashe da alawus din halartar taro a shekarar 2023.
Sauran abubuwa da za a kashe kudaden a kansu sun hada da sayen kyaututtuka, tallace-tallace, duba lafiya, wasanni, aikewa da sakonni, rajista da cibiyoyin samun kwarewa da sauransu.
Hakan kuwa na kunshe ne a daftarin kasafin 2023 da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gabata a makonnin baya.
Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Maguna (NAFDAC) ita ce kan gaba inda ta ware Naira biliyan 7.2 da sunan abubuwa da ke iya bijirowa (Miscellaneous).
Ga jerin hukumomi da cibiyoyin gwamnati da suka samu kaso mai tsoka.
- NAFDAC – Biliyan N7.2
- Hukumar Binciken Haddura (AIB) — Biliyan N2.79.
- Hukuma da cibiyoyi ’yan sanda — Biliyan N2.39
- Jami’ar Legas — biliyan N1.71
- Ma’aiaktar Shari’a — Biliyan N1.56
- Hukumar Kiyaye Haddura — Biliyan N1.55
- Ma’aikatar Wasanni da Harkokin Matasa — Biliyan N1.48
- Jami’ar Ilori — Biliyan N1.43
- Hukumar Binciken Yanayi — Biliyan N1.33
- Fadar Shugaban Kasa — Biliyan 1.11
- Kwalejin Koyon Tukuna Jiragen Sama — Miliyan 950.6
- Ofishin Jakadancin Soji — Miliyan N796.9
- Kwalejin Yaba — Miliyan N757.8.
- Hukumar Kwallon Kafa — Miliyan N753.5
- Hukumar Kula da Hanyoyi — Miliyan N710.3
- Hukumar Ilimin Kasuwanci da Kere-kere — Miliyan N595
- Ofishin Shugaban Ma’aikata — Miliyan N558.6
- Hukumar Shige-da-fice — Miliyan N544.5
- Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Tarayya, Bida — Miliyan N540.7
- Hukumar Sibil Difens — Miliyan N522.9.
‘Hanyar satar dukiyar kasa ce’
Shugaban Cibiyar da ke Sa-Ido kan Ayyukan Majalisa, (CISLAC), Auwal Musa Rafsanjani, ya bayyana cewa kudaden da aka ware almubazzaranci ne kuma babu wani amfani da zai yi wa tattalin arziki da ’yan kasa.
Rafsanjani ya ce, “Abin da ke cikin kasafin maimaici ne da barnar kudin kasa, musamman ganin yadda ake ware kudaden da ake karkatar da dukiyar ’yan kasa.
“Mislai shi ne yadda aka ware makudan kudade wa wasu abubuwa da ’yan Najeriya ke ganin yaudara ce kamar yadda ba sa amfani da ko sisi da ake kashewa kan tallafin mai.”