Sauya takardun kudi zai karya darajar naira – Ministar kudi

0
68

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta soki shirin Babban Bankin Najeriya (CBN) na sauya wasu takardun kudi, tana mai cewa hakan zai iya karya darajar Naira.

Ministar ta bayyana wa Majalisar Dattawa cewa CBN bai shawarci ma’aikatarta kan sauya takardun kudin ba.

“Masu girma sanatoci, CBN bai tuntube  mu a Ma’aikatar Kudi ba kafin daukar wannan mataki na sauya wasu takardun Naira ba, don haka ba za mu iya aron bakinsu mu ci musu albasa ba.

“Amma a matsayina na babbar jami’a a haskar tsare-tsaren kudi a Najeriya, wannan tsarin da ake shirin aiwatarwa a yanzu, na na matukar hadari ga darajar Naira a kasuwar canjin kudade.”

Ministar ta yi wannan jawabi ne a lokacin da take kare kasafin ma’aikatarta a gaban kwamitin Kudade na Majalisar Dattawa a ranar Juma’a.