Za a haramta sayar da motoci masu amfani da fetur a 2035

0
74

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta kulla kafa dokar da za ta haramta sayar da motoci masu amfani da man fetur ko dizel daga shekarar 2035.

Daftarin dokar ta wajabta haramta wa kamfanonin kera manya da kananan motoci yin masu fitar da hayaki gaba daya a 2035.

Babban Mai Shiga Tsakani na Majalisar EU, Jan Huitema, ya ce, “Wannan albishir ne ga direbobi…sabbin motoci marasa hayaki za su kara yin sauki ta yadda kowa zai samu ya kuma mallaka.”

Shugaban shirin yaki da sauyin yanayi na EU, Frans Timmermans, ya ce, “Nahiyar Turai ta shirya komawa amfani da tsarin sufuri marar hayaki,” kuma yarjejeniyar sako ne ga masana’antar kera motoci da kwastomominsu.

Dokar da Wakilai daga kasashen Tarayyar Turai 27 suka tsara za ta hana sayar da motocin da ke amfani da mai a fadin nahiyar.

Manufar dokar ita ce ganin an hanzarta komawa amfani da motoci masu amfani da wutar lanatarki da nufin rage sauyin yanayi.

Hukumar Tarayyar Turai da da Majalisar Tarayyar da wakilan kasashen sun sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Alhamis.