Dalilin da ya sa har yanzu ake fama da karancin mai – IPMAN

0
80

Shugaban Kungiyar Dillalan Man Fetur na Nijeriya (IPMAN), Debo Ahmed, ya ce har yanzu man fetur na kara karanci a Babban Birnin Tarayya, Abuja da kewaye duk da ambaliya da ta haddasa cunkoson ababen hawa a Lakwaja da ke Jihar Kogi ta ja baya, saboda gibin wadatar man da aka samu.

Tun farkon watan Oktoba, an yi dogwayen layukan man fetur da dama a gidajen sayar da mai a Abuja da wasu yankuna.

Hukumar da ke sa ido kan harkokin man fetur a Nijeriya (NMDPRA) ta dora alhakin karancin man kan ambaliyar ruwan da ta yi sanadiyyar mamaye manyan tituna a Lakwaja wanda hakan ne haddasa karancin.

Amma a ‘yan kwanakin nan ambaliyar ruwan ta ragu, sai dai duk da haka karancin man fetur ya ci gaba da wanzuwa a Abuja da kewaye.

Shugaban Kungiyar na IPMAN ya danganta matsalar karancin man da ake samua halin yanzu kan masu kamfanonin da suke dakon man.

“Su (masu kawo kaya) sai sun sauke kayansu daga motoci sannan mutane su saya.

“Mutane da yawa suna tunanin har yanzu akwai batun (karanci) don haka ne ake ci gaba da bin layin mai a gidajen sayar da man. Ba wai babu man bane, akwai mai da yawa a cikin ramukan da suke sayarwa a gidajen man, amma saboda gibin da aka samu na dakon kayayyakin ne ya sa har yanzu karancin man ke dada karuwa,” in ji shi.