Kasashe 10 da suka fi tsananin zafi a duniya a bana

0
92

A ranar Talata 10 ga watan Mayu ne hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta duniya ta yi gargadin cewa duniya na iya fuskantar mummunan yanayin zafi sama da wanda ake gani yanzu a cikin shekaru biyar gaba.

Hukumar ta ce yanayin zai zarta maki daya da digo bayar na gejin da ake kokarin kaucewa kan ma’aunin selsius, wanda kuma ake nuna fargaba a kai.

Masana kimiyya sun ce ko da sau daya a cikin shekara aka samu yanayin da ya zarta maki 1.5, za a shiga yanayi mai mugun hadari da samun narkewar kankara kan teku da ambaliya.

Hukumar ta ce karya dokokin da aka cimma a yarjejeniyar sauyin yanayi na birnin Paris ko da sau guda ne, na iya haifar da matsalar da za a jima ana dandana kuda na dumamar yanayi.

A yanayin da ake cikin tun daga wata Afrilu kasashe irin Nijeriya da makwabtanta ke fuskantar tsananin zafi, ta yadda har wasu ‘yan kasar ke ganin babu kasar da takai tasu zafi.

A wannan mukala, BBC Hausa ta yi Nazari kan kasashen da suka fi zafi a duniya, ta hanyar yin bincike, inda ta samo bayanai daga wata cibiyar bincike mai zaman kanta a Amurka kan abubuwan da suka shafi al’amuran duniya wato World Population Review.

A shafinta na intanet, cibiyar ta wallafa kasashen da suka fi tsananin zafi a shekarar2022, wanda Nijeriya ba ta bayyana ma a cikin goman farko ba.

Matakin farko da ake bi wajen tantance kasar da ta fi kowacce zafi a duniya shi ne aunata.

Misali shin kasar ita ce wadda ta fi kowacce tsananin zafi a duniya a shekarar da ta gabata? Idan haka ne, wannan ita ce Kasar Kuwait, wadda tsanain zafi ya kai maki 53.2 a ma’aunin selshiyos a Birnin Nuwaiseeb a ranar 22 ga watan Yunin 2021.

Shin ita ce kasar da ta sanar da tsananin zafi mafi kuna a tarihi? Idan haka ne, wannan kasa ita ce Amirka, da zafin ya kai maki 56.7 a ma’aunin salshiyos a Death Valley, a Californias a shekarar 1913.

Shin wannan kasar ita ce ta fi kowacce zafi a lokacin bazara, ba tare da la’akari da sanyin da aka yi a lokacin hunturu ba? Ita ce kasar da yanayin zafin ya zama babu yabo ba fallasa cikin shekaru 30 da suka gabata? Bayan duba duk wadannan abubuwa, wannan mukala za ta yi Nazari akan kasa ta karshe da muka ambata.

Kasashe 10 da suke sahun gaba a matsanancin zafi a duniya daga shekarar1991-2020 ( ta amfani da madaidaicin yanayin zafi a kowacce shekara).

Mali – Zafin ya kai maki 28.83°C/83.89° F a ma’aunin selshiyos.

Burkina Faso – Zafin ya kai maki 28.71°C/83.68° F a ma’aunin selshiyos.

Senegal – Zafin ya kai maki 28.65°C/83.57° F a ma’aunin selshiyos.

Tuvalu – Zafin ya kai maki 28.45°C/83.21° F a ma’aunin selshiyos.

Djibouti – Zafin ya kai maki 28.38°C/83.08° F a ma’aunin selshiyos.

Mauritania – Zafin ya kai maki 28.34°C/83.01° F a ma’aunin selshiyos.

Bahrain – 28.23°C/82.81° F a ma’aunin selshiyosPalau – Zafin ya kai maki 28.04°C/82.47° F a ma’aunin selshiyos.

Katar – Zafin ya kai maki 28.02°C/82.44° F a ma’aunin selshiyos.

Gambia – Zafin ya kai maki 27.97°C/82.35° F a ma’aunin selshiyos.