Mambobin APC sama da 200 sun sauya sheka zuwa PDP a Kebbi

0
75

Akalla mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 216 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a yankin Kofar Kola da ke Birnin Kebbi, babbar birnin jihar Kebbi.

Jam’iyyar APC na da karfi sosai a garin Kofar Kola saboda kasancewarsa yankin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu.

Wadanda suka sauya shekar zuwa PDP da suka hada da maza 134 da mata 84 sun kasance mambobin jam’iyyar mai mulki a yanki.

Manyan shahararrun yan siyasa a cikinsu sun hada da Alhaji Atiku Bandado, Alhaji Gwandu Mai Kifi, Alhaji Yahaya Lele, tsohon hadimin gwamnan.

Sai kuma Alhaji A.M. BK, wanda ya kasance tsohon shugaban kwalejin ilimi na Adamu Augue da ke jihar.

Masu sauya shekar sun samu tarba daga dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar, Janar Aminu Bande mai ritaya.

Sauran wadanda suka yi masu lale marhaban sun hada da darakta janar na kwamitin yakin neman zaben gwamnan, Alhaji Abubakar Shehu, sakataren labaran jam’iyyar, Alhaji Sani Dododo da kuma sauran jiga-jigan PDP a jihar.