Dubun mata da mijin da ke safarar mutane ta cika a Ogun

0
79

Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun, ta damke wasu ma’aurata Godday da Ebere Samuel bisa zarginsu da safarar mutane a Atan da ke yankin Ota a jihar.

Kakakin yan sandan jihar, SP Abimbola Oyeyemi, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Ota, inda ya ce an kama ma’auratan ne a ranar 17 ga watan Oktoba bisa zarginsu da laifin.

Oyeyemi ya ce an kama su ne bayan rahoton da wani Adeniji Okikiolu ya gabatar a hedikwatar yan sanda ta Atan Ota, inda ya bayyana cewa yarsa mai shekara 16 mai suna Maria Adeniji ta bace a ranar 16 ga watan Oktoban 2022.

Ya kara da cewa yayin da aka shiga nemanta, wani ya shaida masu cewa an ga yarinyar da ta bace tare da Ebere.

“Bayan bayanin, an gayyaci Ebere ofishin yan sanda, amma ta musanta cewa ta taba ganin yarinyar da ta bace.

“Rashin gamsuwa da bayaninta ya sa aka tsare ta a caji ofis din.

“Amma abin mamaki, lokacin da aka tuntubi mijinta, ya amsa cewa ya tafi da yarinyar da ta bace zuwa wani wuri a Legas don tafiya Burkina Faso, inda za ta yi aikatau a wajen abokan aikinsu.

“Bincike ya nuna cewa ma’auratan sun dade suna sana’ar safarar mutane kuma abokan aikinsu na can Burkina Faso,” inji shi.

A halin da ake ciki, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika wadanda ake zargin zuwa Sashen Yaki da Fataucin Mutane na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da su a gaban kotu.