Hukumar Kwastam ta kama kayan fasakauri daban-daban har 132 cikin kwanaki 60

0
81

Hukumar Kwastam ta Najeriya (FOU) shiyyar ‘B’ mai hedikwata a Kaduna, ta ce, ta kwace kayayyaki daban-daban har 132 da akayi fasakwarin su da darajar kudinsu ya kai Naira N690,821,657.94 a cikin kwanaki 60 da suka gabata.

Kwanturola Albashir Hamisu wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai jim kadan bayan baje kolin kayayyakin da aka kwace daga jihohin yankin, ya yabawa rundunar sojin Nijeriya bisa gudunmawar da suka bada wajen samun nasarar bankado masu fasakwaurin.

Ya ce, duk da cewa ’yan fasakwaurin suna amfani da kwarewa, amma duk da haka, hukumar kwastam ta kan iya gano su, kuma za ta ci gaba da kwace kayayyakin su har sai sun daina yi wa Tattalin Arzikin kasa zagon kasa.

Kayayyakin da aka kama sun hada da dilar kayan gwanjo 758 da buhunan shinkafa 749 (50kg) ta kasar waje da wasu buhunan shinkafar kasar waje 65 (25kg) da katan 533 na taliyar kasashen waje da macaroni da kuma katon 473 na kayayyakin magunguna na kasashen waje.

Sauran kayayyakin sun hada da fakiti 70 na tabar wiwi da jarika 59 (5 lita) na man gyada da buhuna 47 na takin kasashen waje (NPK 50:50:50) da gwanjon tayoyin mota 245 da jarkar man fetur 221 (25lita) ) da katan 116 na takalman mata na kasashen waje da jarkar man gyada 10 (25lita).

Haka kuma, anyi baje kolin motoci guda 24 da suka hada da guda 4 da aka yi amfani da su wajen jigilar kayayyakin da kuma motocin hawa 20 da katan 14 na man gyaran jiki na kasashen waje da katan 12 na tabar sigari da buhu 39 na gwanjon takalma da buhu biyu na gwanjon jakunkuna.