Jirgin Birtaniya ya dawo da tashi a Abuja

0
74

Jirgin saman kasuwanci na Birtaniya da ya dakatar da jigilar da ya saba ta fasinjoji daga Abuja zuwa Landan ya dawo da jigilarsa.

Jaridar Daily Trust ce ta fara bayar da labarin cewa jirgin mai lamba BA83 ya soke zuwansa Abuja a ranakun Juma’a da Asabar, awanni 24 bayan ya karkata saukarsa zuwa Legas.

Wakilinmu ya rawaito cewa jirgin mai lamba BA83 wanda zai tashi daga Abuja zuwa Landan a ranar Alhamis, kwatsam aka karkatar da shi zuwa Legas.

Wannan mataki ya fusata fasinjoji masu tafiya kasashen waje, inda suka rika kokawa da cewa kamfanin jirgin bai sanar da su daukar wannan matakin ba.

Sai dai karkatar da jirgin zuwa Legas ba zai rasa nasaba da gargadi na yiwuwar aukuwar hare-haren ta’addanci da Ofishin Jakadancin Amurka ya yi ba a makon jiya.

Kwanaki biyu bayan kurar gargadin ta lafa ne sai ga shi kamfamin ya dawo da sauka da tashi daga Abuja daga ranar Lahadi 30 ga wtan Oktoba zuwa 7 ga watan Nuwamba.

Daga yanzu jirgin zai rika tashi daga Abuja ne da karfe 8:00 ya kuma sauka a filin jirgin sama na Heathrow da ke Landan da karfe 6:25 na yamma.