Gobara ta yi ajalin mutane shida a Legas

0
85

Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar yau a unguwar Adeola Odeku da ke Victoria Island, Legas, ta yi ajalin mutane akalla shida.

Gobarar ta kone wani gini da ake zargin wani banki ne, sannan an kuma ga motoci suna ci da wuta.

Mutanen dake kusa da gurin sun kori ‘yan kwana-kwana a otal din Eko Suites da jifan duwatsu.

Har zuwa lokacin da ake wannan rahoto, ba a bayyana ko an shawo kan barkewar gobarar ba.