Dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar NNPP, Rabiu Musa ya shelanta cewa, wasu daga cikin kadarorinsa ya sayar ya dauki nauyin karatun wasu daga cikin daliban jihar zuwa karo karatunsu zuwa kasashen waje.
Kwankwanso ya sanar da hakan ne a jawabinsa a gurin taron karrama shi da kungiyar Kwankwasiyya tare da hadaka da majalisin masu ilimi suka gudanar a Abuja.
A cewar Kwankwanso, bayan ya bar gidan gwamnatin Jihar Kano a matsayin gwamna, ya sayar da kadarorinsa da ba ya bukata domin daukar nauyin karatun daliban, inda ya nuna jin dadinsa kan yadda ya dauki nauyin karatun dalibai 3,000 da suka amfana a cikin shekaru hudu.
Ya kara da cewa, an ba shi kwarin gwiwar kirkiro daukar nauyin karatun daliban maza da mata, inda ya sanar da cewa, âbayan mun wallafa tallan na daukar nauyin karatun a 2019 mutane âyan kadan ne aka samu suna da babban mataki na karatu kuma mun yi amfani da su haka kuma mun yi amfani da wasu daliban masu matakin karatu na biyu wadanda su ma aka dauki nauyin karo karatunsu.
âMuna da sama da dalibai 3,000 da suka je kasashen duniya 14, saboda haka na ji dadi matuka wajen daukar nauyin karatunsu.
âSama da dalibai 412 ne suka amfana, inda kuma sama da 3,000 aka tura su zuwa kasar waje karo karatun.
âIna ganin abin da ya fi dacewa ko wanne dan siyasa ya yi shi ne, ya zuba jari mai yawa a fannin ilimin zamani domin ta haka ne kawai, kasar nan za ta bunkasa.
âA lokacin ina matsayin gwamna, mun samu nasarar ciyar da daliban makarantun firamare na gwamnati na jihar.â
A nasa jawabin a gurin taron, shugaban kungiyar ta Kwankwasiyya, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya bayyana cewa, jinjina wa kokarin na Kwankwaso ne dan takarar, musamman wajen inganta rayuwar talakawa.