Masarauta ta hana cin kasuwa saboda hare-haren ‘yan bindiga a Neja

0
85

Masarautar Borgu da ke Jihar Neja ta bayar da umarnin rufe wasu manyan kasuwanni saboda hare-haren ‘yan bindiga.

Masarautar ta bayar da umarnin rufe kasuwannin ne saboda fargabar kai harin ‘yan bindiga a yankin.

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na kungiyar ci gaban matasan Borgu, Muhammad Kabir ya fitar a madadin masarautar, ya ce an dauki wannan mataki ne a wani taro na gaggawa a ranar Litinin.

“An rufe dukkannin kasuwannin har sai abin da hali ya yi, amma mutum zai iya sayen dan abin bukata a kusa da shi a cikin lokacin da aka ware….” a cewar sanarwar

Sanarwa ta ci gaba da cewa, an hana yawon talla gida-gida da kuma na kan titi. Duk wani saye da sayarwa an haramta sai dai a yi shi a kasuwa.

Haka kuma duk wani mai abin hawa dole ne ya tabbatar yana da lamba, ko kuma a kwace daga ranar Litinin ta makon gobe.

Kazalika, sanarwar ta ce masu sana’ar daukar fasinja a babur dole ne su sa rigar falmaran mai daukar haske da za a iya shaida mutum.

Sanarwar ta kuma ce, dukkannin wadannan matakai na wucin gadi ne, kuma za a sake duba su, daidai da bukatar da ta taso.

Umarnin rufe kasuwanni da daukar wadannan matakan na zuwa ne bayan hari da aka kai barikin sojoji da ke Wawa kusa da Madatsar Ruwa ta Kainji