Dalilin da yasa na fi Atiku da Obi sanin tattalin arziki – Tinubu

0
146

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, da mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, a ranar Talata, sun caccaki ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da na LP, Peter Obi,  ya ce basu da tarihi da gogewa wajen jagorantar kasar nan.

Ya yi magana ne a lokacin da yake gabatar da shirin aikinsa a gaban ‘yan kasuwa da kamfanoni masu zaman kansu a Legas a jiya Talata.

‘Yan kasuwar sun samu cikakken wakilcin shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote; Shugaban bankin Zenith, Jim Ovia; Shugaban UBA, Tony Elumelu; tsohon shugaban bankin Access, Aigboje Aig-Imoukhuede; Babban jami’in rukunin na bankin Access, Herbert Wigwe, da sauran shugabannin ‘yan kasuwa masu wakiltar kungiyoyi irin su noma, mai da iskar gas, da bangaren kasuwannin masana’antu, fannin kere-kere, da dai sauransu.

Taron ya samu halartar dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima; Gwamna Babajide Sanwo-Olu (Lagos); Simon Lalong (Plateau); Atiku Bagudu (Kebbi); Abdulrahman Abdulrazaq (Kwara), Abubakar Badaru (Jigawa); Dapo Abiodun (Ogun); Adegboyega Oyetola (Osun); Nasir El-Rufai (Kaduna); da Abdullahi Ganduje (Kano) da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar APC.

Da yake jawabi a wurin taron, tsohon gwamnan na Legas ya ce idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023, gwamnatinsa za ta samu riba mai yawa a cikin gida biyu.

A cewar wata sanarwa da ofishin yada labarai na Tinubu, mai dauke da sa hannun Tunde Rahman, dan takarar shugaban kasar ya bayyana cewa, samun nasarar hakan na iya yiwuwa ya samu irin wannan nasarar ta fuskar tattalin arziki a lokacin da yake mulkin jihar Legas.

Ya yi kira da a tallafa wa ’yan kasuwar Legas, inda ya bayyana cewa ana bukatar hakan ne domin samun ingantaccen tattalin arziki.