Netanyahu na gab da yin nasara a zaɓen Isra’ila

0
114

Tsohon Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na kan hanyar samun nasara a babban zaben kasar da aka gudanar, kamar yadda sakamakon ra’ayin wadanda suka kada kuri’a ya nuna.

Hasashen ya nuna cewa Mista Natenyahu na kan gaba da ‘yar tazara a yawan kujerun da jam’iyyarsa za ta samu a majalisar dokokin kasar.

Wannan sakamako na hasashen dawowar Mista Netanyahu kan karagar mulkin da ya rasa iko da shi ne a shekarar da ta gabata bayan shafe shekara 12 a jere yana jagorantar kasar.

Netanyahu ya faɗa wa cincirindon magoya bayansa a birnin Kudus cewa ”muna dab da samun babban nasara”.