‘Yar Najeriya ta zama birgediya janar din sojin Amurka

0
106

Wata soja ‘yar asalin Nijeriya, Amanda Azubuike ta samu karin girma daga mukamin Laftanar-Kanar zuwa Birgediya-Janar na Sojin Amurka a sansanin soji da ke Fort Knox, Kentucky, a Amurka.

Azubuike, haifaffiyar Landan wadda mahaifanta ‘yan Nijeriya ne, ta shiga aikin sojan Amurka a 1994, inda ta zama jami’a a fannin jirgin sama bayan ta kammala kwas din tukin jirgin sama a Kwalejin Koyon Tukin Jirage ta Sojoji.

A cikin sakon taya murna a shafin Twitter, Manjo-Janar Antonio Munera ya ce: “Ina taya murna ga sabuwar USACC da ta samu ci gaba, Birigediya-Janar Amanda Azubuike! a yau, ta karbi tauraruwarta ta 1 daga Janar James Rainey,  yayin wani biki tare da dangi, abokai, da shugabannin al’umma.

Azubuike ta yi aiki a matsayin mataimakiyar kwamandan rundunar sojin Amurka ta Cadet kuma a baya ta zama Babbar Hafsan Hafsoshi da Babbar Mai Bada Shawara kan Soja a Ofishin Sakataren tsaro.

Ta kuma kasance Shugabar Hulda da Jama’a a Kudancin Amurka, a yankin Fort Lauderdale, da Daraktar Hulda da Jama’a, Hadin gwiwar Rundunar HQs-‘National Capital Region/Military District ta Washington DC.

Ta kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara ta sadarwa don kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa ta kasa da kuma ma’aikaciyar Hulda da Jama’a ta kungiyar NFL, Washington Redskins.

Azubuike ta na da digiri na farko a Kimiyya a harkar sadarwa da ilimin kafafen yada labarai a Jami’ar Central Arkansas, Jagoran Fasaha a Tsaron Kasa da Nazarin Dabaru daga Kwalejin Yakin Sojin Amurka, kuma Jagora ce ta Nazarin Kwararru, Hulda da Jama’a da Sadarwar Kasuwanci daga Jami’ar Georgetown.