Adawar siyasa: ‘Yan siyasa sun fara kewaya wa junansu Al-kur’ani a Yobe

0
105

Masu iya magana sun ce: siyasa ba da gaba ba, wanda ana iya cewa hakan ya saba lamba a Yobe ta Arewa, yayin da adawar siyasa ta dauki sabon salo tsakanin magoya bayan manyan yan siyasar yankin, al’amarin da ya kai ga zagayawa juna Al-Kur’ani Mai Girma tare da yanka saniya domin tona asirin wani da daya bangaren adawar ke zargin namiji ne ya bude a Facebook wanda suke zargin yana cin zarafin mai gidansu a siyasa.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu a jihar cewa, akwai bangarori uku, wadanda basu ga-maciji da juna, wanda sun dade suna kai ruwa rana tare da jifar juna da miyagun kalamai, sannan kuma dukan su ya’yan jam’iyyar APC mai mulkin jihar ne.

Bugu da kari kuma, majiyar ta kara da cewa, an samu wannan baraka ne tun bayan fitowar da hadimin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya yayi na takarar kujerar Majalisar Wakilai a Kananan Hukumomin Bade da Jakusko- Hon. Sani Ahmed Kaitafi, kana da bahallattsar da ta kaure tsakanin Sanata Lawan da Bashir Machina a takarar Sanatan Arewacin Yobe.

Adawar siyasa ta kara tsami ne a yan kwanakin nan sakamakon wani rubutun da wata mai ta’ammuli da turakar Facebook mai suna ‘Maryam Yusuf Dachiya’ ta yi wanda ya dada rura wutar adawar, wadda daya bangaren ya yi zargin cin zarafin Kwamishina a Ma’aikatar Kasafin Kudi a jihar Yobe, Hon. Muhammad Gagiyo wanda ya kai ga daukar matakin sauke Al-Kur’ani Mai Girma tare da yanka saniya domin tona asirin wanda ake zargin.

LEADERSHIP ta tuntubi Mallam Ibrahim Babagana, Shugaban kungiyar ‘Gagiyo Youths Banguard’ da ke Gashu’a, dangane da makasudin kewaya Al-Kur’anin wanda ya fara da bayyana cewa, “Ba kewaya Al-Kur’ani muka yi ba, face kawai mun gayyato manyan mallammai da ke cikin garin Gashu’a domin mu karanta Al-Kur’ani Mai Girma tare da yanka saniya matsayin sadaka da nufin Allah ya tona asirin wanda ya kirkiri turakar Facebook mai suna ‘Maryam Yusuf Dachiya’. Saboda yadda mai wannan sunan ya fake yana cin zarafin manyanmu.”

“Mun dauki wannan matakin ne ta hanyar gudanar da addu’ar Allah ya tona asirin sa da duk wanda yake goya masa baya. Musamman abin da ya faru kwanan nan inda mai wancan turakar ya yi wa jagoranmu, Hon. Muhammad Gagiyo kazafin da ya saba da al’ada da addinin musulunci. Saboda a matsayin Hon. Kwamishina, mutum ne mai mutunci kuma yana da iyalai, yan uwa da surukai, ace irin wannan zai faru kuma ayi shuru, sam bai dace ba.” In ji shi.

Mallam Babagana ya ce, ba yanzu ne hakan ya sha faruwa ba, wajen amfani da kafofin sada zumunta a yi wa dattawa da manyan mutane masu daraja kazafi ko cin mutunci. Ya ce, “Abin ne yayi yawa, kuma mun ga ya dace mu dauki tsauraran matakan shawo kan wannan matsalar.” Ya nanata.

Tuni dai wannan matakin ya jawo cece-kuce tare da rabuwar kawuna, inda wasu ke kallon matakin yayi tsauri, tare da ishara da cewa haka siyasa ta gada, yayin da wasu ke ganin hakan ya dace saboda gani ga wane ya ishi wane wa’azi.

Har wala yau, wasu kuma kira suka yi ga bangarorin da cewa a kai zukata nesa tare da yin adawar siyasa mai tsabta, tare da kiran bai-daya ga shugabannin siyasar Arewacin Yobe, da ma jihar baki daya cewa su rinka kaffa-kaffa da kalaman da ya dace suna furtawa, kana su ja kunnen magoya bayansu da yi musu tilawar muhimmancin zaman lafiya.