Mutum 3 sun mutu a saukar gaggawa da jirgin sama ya yi cikin kogi

0
104

An tabbatar da mutuwar mutum uku sakamakon saukar gaggawa da wani jirgin fasinja ya yi a cikin Kogin Victoria na Tanzaniya a safiyar Lahadi.

Hukumomi sun bayyana cewa zuwa yanzu an yi nasarar ceto mutum 26 daga cikin 43 da ke cikin jirgin na Precision Air.

Har yanzu ba a kai ga gano inda 14 suke ba.

Jirgin ya taso daga Dar es Salaam, babban birnin Tanzaniya, zuwa Bukoba É—auke da fasinja 39.

Hukumomi sun zargi mummunan yanayi da haddasa hatsarin.