Na shiga wani yanayi mai wuya a lokacin da zan buga fenariti – Haaland

0
89

Manchester City ta doke Fulham da ci 2-1 a wasan mako na 15 a gasar Premier League ranar Asabar.

City ce ta fara cin kwallo a minti na 17 da fara wasa ta hannun Julian Alvarez daga baya Fulham ta farke ta hannun Andreas Pereira a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Daf da za a tashi wasan City ta samu fenariti, sannan Erling Haaland ya buga ya kuma ci, duk da mai tsaron raga Bernd Leno ya yi kokarin tare ta.

Mai shekara 22 ya yi murna kan kwallon da ya ci kuma na 18 a kakar nan, dan wasa na biyu da ya zura kwallo a wasa shida a gida a jere, bayan Alvaro Negredo a 2013.

To sai dai dan kwallon ya sanar da Sky Sports cewar ”Gabana ya fadi – yanayin da gabana ya fadi sosai kenan a tarihin rayuwata.

Fenariti a lokacin daf a tashi daga wasa? Hakila dole na shiga damuwa,” kamar yadda ya sanar da BBC. ”Yanayi ne na bukatar natsuwa ka samar da abin da ake bukata kuma abin da na yi kenan, jin dadi mai yawa idan ka zura kwallo a raga.

”Na yi jinya makonni, kuma abu ne mai mahimmaci a tare da mu da muka yi nasara.”

Tun farko Haaland wanda ya fara karawar a kan benci ya ci kwallo da ka daga bayan da ya shiga wasan, amma VAR ta soke da cewar an yi satar gida.

Kawo yanzu Haaland ya zura kwallo 18 a Premier League a wasa 12, kuma na 23 a karawa 17 da ya yi wa City a dukkan fafatawa a kakar nan.