Ya kamata CBN ya sanya hoton Obasanjo a jikin sabbin kudin da za a sauya wa fasali – Atiku

0
104

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bukaci Babban Bankin Nijeriya (CBN), da ya sanya hoton tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo a kan takardun kudin Naira da aka shirin sauya wa fasali.

Atiku ya ce ya kamata fuskar Obasanjo ta kasance a kan kudin saboda kokarin da ya yi na ganin Nijeriya ta zauna kan saiti.

Dan takarar shugaban kasar na PDP, ya ce samun hoton Obasanjo a kan Naira zai kara zaburar da al’ummar Nijeriya nan gaba wajen sadaukarwa ga kasar nan.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku ya rubuta cewa: “Afirka na da albarka da samun shugaban kasa mai kishin dimokuradiyya kamar Obasanjo.

“Mutumin da ya kamata hotonsa ya kasance a kan takardar Naira da aka shirin sauya wa fasalin domin zaburar da al’ummar Nijeriya da su sadaukar da kansu ga al’ummarsu da nahiyarsu.”

A kwanakin baya ne gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya sanar da shirin sake fasalin kudin N100, N200, N500, da N1000.

Gwamnan na CBN, ya ce za a fitar da sabbin takardun ne a ranar 5 ga Disamba, 2022.