Ranar Litinin za a raba jadawalin Champions League, wasannin zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a gasar bana.
Za a raba wadanda suka kai zagyen gaba zuwa rukuni biyu, na farko wadanda suka yi na daya a rukuninsu da na biyu wadanda suka yi na bibiyu a kowanne rukuni.
Jerin wadanda suka yi na daya a kowanne rukuni: Bayern, Benfica, Chelsea, Manchester City, Napoli, Porto, Real Madrid da kuma Tottenham.
Wadanda suka yi na bibiyu a kowanne rukuni: Club Brugge, Dortmund, Frankfurt, Inter, Leipzig, Liverpool da kuma Milan, Paris St Germain.
Yadda za a raba jadawalin tsakanin kungiyoyin 16:
Kungiyar da ta kara da wata a rukunin farko ba za su hadu ba a zagaye na biyu.
Kungiyoyi daga kasashe daya ba za su hadu ba a wasan zagaye na biyu.
Wadanda za su iya haduwa a zagaye na biyu:
Wadanda suka ja ragamar kowanne rukuni
Bayern ( Daga Jamus)
Watakila a hada ta da daya daga: Club Brugge, Liverpool, Milan, Paris
Ba za ta fuskanci Dortmund ko Frankfurt ko Inter ko kuma Leipzig ba
Benfica (Daga Portugal)
Wadanda za ta iya fuskanta: Club Brugge, Dortmund, Frankfurt, Inter, Leipzig, Liverpool, Milan
Ba za ta kara da Paris St Germain ba
Chelsea (Daga Ingila)
Wadanda za ta iya karawa da su: Club Brugge, Dortmund, Frankfurt, Inter, Leipzig, Paris
Ba za ta yi wasa da Liverpool ko kuma Milan ba
Manchester City (Daga Ingila)
Wadanda za ta iya fuskanta: Club Brugge, Frankfurt, Inter, Leipzig, Milan, Paris
Ba za ta fafata da Dortmund ko Liverpool
Napoli (Daga Italiya)
Za ta iya fuskantar daya daga: Club Brugge, Dortmund, Frankfurt, Leipzig, Paris
Ba za ta kara da da Inter ko Liverpool ko kuma Milan ba
Porto (Daga Portugal)
Wadanda za ta iya karawa tsakanin: Dortmund, Frankfurt, Inter, Leipzig, Liverpool, Milan, Paris
Ba damar ta kara da Club Brugge
Real Madrid (Daga Sifaniya)
Za ta iya fuskantar daya daga cikin: Club Brugge, Dortmund, Frankfurt, Inter, Liverpool, Milan, Paris
Ba damar a hada ta da Leipzig
Tottenham (daga Ingila
Watakila a hada ta da daya daga cikin: Club Brugge, Dortmund, Inter, Leipzig, Milan, Paris
Ba damar ta kara da Frankfurt ko kuma Liverpool.