‘Ya’yan jam’iyyar PDP sama da 1,000 sun sauya shekar siyasa zuwa APC a Zamfara

0
265

Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta karbi ‘ya’yan jam’iyyar PDP sama da 1,000 da suka sauya sheka.

Jam’iyyar ta sanar da sauya shekar ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam’iyyar na jihar, Yusuf Idris Gusau.

A wani bangare na takardar, “Ficewar shugabar mata ta jam’iyyar PDP ta jihar, Hajiya Madina Shehu, da mata sama da 1,000, ciki har da masu gudanar da yakin neman zaben jam’iyyar PDP, wani ci gaba ne na maraba ga jam’iyyar mu a zabe mai zuwa.

“sauya shekar ‘ya’yan Jam’iyyar PDP zuwa APC ya maida PDP a jihar cikin wani hali mawuyaci na rashin tsari wanda hakan ya kara wa jam’iyyar APC damar lashe zabe a duk matakan siyasa na jihar.