Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jamâiyyar LP, Mista Peter Obi ya sha alwashin tabbatar da zaman lafiya da gyara tattalin arzikin Nijeriya idan aka zabe shi ya zama shugaban kasa a shekarar 2023.
Mista Obi ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci Jihar Nasarawa domin gangamIn yakin neman zaben 2023.
Dan takarar ya ce Nijeriya tana fama da matsaloli ciki har da rashin tsaro wanda ya fi addabar alâumman kasar, ga kuma matsalar rashin aikin yi da ya sa wahalhalu, musamman a tsakanin matasa.
Obi ya ce jamâiyyar LP za ta samar da ayyukan yi ga matasa domin magance zaman kashe wando. Ya kara da cewa zai hada kan âyan Nijeriya saboda su zama tsitsiya madaurinki guda.