Wata kotun majistare a jihar Kano ta yi wa wasu matasa masu wallafa hotunan bidiyo a dandalin sada zumunta na Tiktok da Facebook bulala ashirirn-ashirin tare da hukuncin biyan tara ta naira dubu ashirin kowannensu da kuma share kotun na tsawon wata guda.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta same su da laifin bata sunan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kokarin tada fitina a cikin al’umma, sannan kuma kotun ta umarcesu su koma kan dandalin na tiktok din su yi bidiyon bai wa gwamna Ganduje hakuri kan bata masa suna.
Matasan Mubarak Isa Muhammad da aka fi sani da Mu, da Nazifi Muhammad Bala, na shirya gajeren bidiyon barkwanci, inda akasari suke kwaikwayon muryoyin wasu fitattun mutane.
Mabarak Unique Pidkin da abokinsa za kuma su share harabar kotun Norman Silance baki dayanta har na tsawon wata guda.
Lauyan da ya shigar da kara Barista Wada Ahmed Wada, ya shaida wa BBC cewa, na gurfanar da matasan ne a gaban kotun saboda laifukan da suka hada da bata sunan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kuma kokarin tayar da fitina,
Inda kuma suka amsa laifinsu al’amarin da yasa aka yanke musu hukuncin, Lauya mai gabatar da kara ya ce an kama matasan tun makon jiya inda aka gurfanar da su a gaban kotun, kafin daga bisani kuma aka aika su gidan yari.
Matasan dai suna hannun jami’an tsaro har sai sun cika wadannan ka’ido kafin a sake.
Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzirci shi ne lauyan matasan ya kuma gode wa kotun majistaren bisa sassaucin da ta yi musu game da hukuncin, don haka ma basu kalubalanci hukuncin ba.