A ranar Litinin dinnan ce Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) za ta yi taron gaggawa domin cim-ma matsaya kan sake tsunduma yajin aiki kan zaftare albashin watan Oktoba da Gwamnatin Tarayya ta biya mambobinta.
Majalisar Zartarwa (NEC) ta ASUU ta kira taron ne a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke shirin biyan albashin wata taskwas ga malaman jami’a da suka balle daga ASUU, wadda ta shafe wata takwas tana yajin aiki a baya.
Aminiya ta ruwaito wani jami’in ASUU da ya nemi a boye sunansa, yana cewa, “NEC din ASUU za ta yi zama a ranar Litinin 7 ga Nuwamba don cim-ma matsaya kan shiga sabon yajin aiki, saboda rabin albashin da aka biya mu a Oktoba.
“ASUU ta fusata da abin da Gwamnatin Tarayya ta yi, don haka za ta yanke shawara a ranar 7 ga watan Nuwamba,” in ji shi ta wayar tarho a karshen mako.