Buhari ya jajanta wa ‘yan kasuwar sinadarai ta Onitsha

0
129

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya jajanta wa ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a iftila’in gobarar da ya auku a kasuwar sinadarai da ke Karamar Hukumar Onitsha ta Jihar Anambra.

Cikin sakon ta’aziyyar da ya aika wa iyalan marigayan ta hannun mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ranar Laraba a Abuja, Buhari ya taya ‘yan kasuwar da suka tafka asara sakamakon fashewar jimamin abin da ya same su.

Daga nan ya yi fatan samun waraka ga wadanda suka jikkata a iftila’in.

Shugaban ya yi amfani da damar wajen kira ga hukumomin da lamarin ya shafa da su gaggauta kai wa wadanda lamarin ya shafa tallafin da ya dace

Haka nan, ya bukaci jami’an tsaro da su zurfafa bincike da zimmar hana aukuwar haka a gaba.

Bayanai sun ce gobarar ta tashi a kasuwar ne ranar Talata da misalin karfe 12:00 na rana bayan da sinadaran da ke tattare a shaguna suka soma fashewa.