Na sanar da sarki Charles III ba ni da gidan kaina a Birtaniya – Buhari

0
129

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya sanar da Sarki Charles na III cewa ba shi da gidan kansa a duk fadin Birtaniya.

Aminiya ta ruwaito cewa, Buhari ya sanar da sarkin hakan ne yayin da ya kai ziyara Fadar Buckingham a ranar Laraba.

Yayin da yake ganawa da ’yan jarida bayan ziyarar da ya kai wa sarkin mai shekara 73, ya ce sarkin ya tambaye shi ne ko yana da gidan kansa a Birtaniya.

sai dai Buhari ya ce makusudin ziyarar ita ce tattaunawa kan alaka tsakanin kasashen biyu ta fuskar kasuwanci da diflomasiyya.

Ya ce an tsara ganawar ta su ce a baya a Kigali tun kafin ya zama sarki, sai dai a wannan lokaci ne ganawar ta tabbata.

Wannan ce ganawa ta farko tsakanin shugaba Buhari da basaraken tun bayan hawan sa kan karagar mulki.

Bayanai na cewa ganawar ta bai wa shugaban na Najeriya damar taya sarkin murnar hawa mulki.