Wata mata ta shafe watanni 6 tana sayar da zobon da ta hada da jinin cutar kanjamau

0
104
Wata mata da kawo yanzu babu wani cikakken bayani a kanta ta bayyana cewa tana amfani da jini mai dauke da kwayoyin cutar kanjamau wajen hada zobon da take sayarwa jama’a.

Matar wadda ta yi wannan ikirari ta bayyana hakan a yayin wani shiri mai taken hada-hadar kasuwanci na MarketRunz da gidan rediyon Wazobia FM ya saba watsawa a duk daren ranar Laraba.

A cikin shirin dai masu sauraro kan kira ta lambar waya su fadi ababen da suke aikatawa a bayan fage kan harkokinsu na kasuwanci wadanda abokan huldarsu ba su da masaniya a kai, duk da cewa sukan yi hakan ne ba tare da wani alfahari ba.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, matar ta ce babbar manufar wannan aika-aika da take yi ita ce yada wannan cuta mai karya garkuwar jiki a tsakanin al’umma.

A cewar wannan mata, “na je aisiti watanni shida da suka gabata sai aka sanar mani da cewa ina dauke da cutar HIV.

“Ba ni da kudin da zan yi maganin wannan cuta don haka na yanke shawarar ba zan bari na mutu ni kadai ba sai dai a yi mutuwar kasko.

“A bisa wannan shawara da na yanke ce na soma zuba jinin jikina a cikin zobon da nake hadawa ina sayar wa mutane masu tarin yawa.

“Nakan samu sirinji na zuko jinin sai na hada zobon da shi. Ni malamar asibiti mai aikin jinya amma bayan na samu tabbacin ina dauke da wannan cuta sai na daina zuwa aikin.

“Ba na murna da wannan abu da nake aikatawa amma ina cike da farin cikin cewa ba zan mutu ni kadai ba.

“A yanzu watanni shida ke nan ina wannan abu kuma ina addu’a Allah zai yafe min.