Gwamnan Bauchi ya amince da fitar da miliyan 500 don biyan giratuti

0
123

Shugaban Ma’aikatan Jihar Bauchi, Alhaji Yahuza Adamu Haruna, ya sanar da cewa gwamnatin jihar ta amince da fitar da Naira miliyan 500 domin biyan kudin giratuti cikin hanzari.

Adamu ya bayyana cewa, Gwamna Bala Muhammad, ya amince da biyan kudin a yayin zaman majalisar zartaswa na jihar da ya gudana a ranar Juma’a.

Da yake magana da manema labarai ranar Juma’a, Yahuza ya bayyana cewa gwamnatin jihar tana aiki tukuru domin biyan dukkanin hakkin tsofafin maikatan jihar.  Yahuza ya kara da cewa an fitar da sabon tsarin biyan hakkin tsofafin maikata a kwanakin baya wanda tuni Gwamna Bala ya sa hannu.