Sauyin yanayi: Kasashen Turai munafukai ne – Buhari

0
109

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna yatsa ga Kasashen Yamma yana mai kiran su da “munafukai” saboda gazawarsu wajen daukar matakan da suka dace kan sauyin yanayi.

“Da yawa daga cikin takwarorina [Shugabannin Kasa] na nuna damuwa game da munafurcin kasashen Yamma da gazawarsu wajen kasa daukar matakin da ya dace,” a cewar shugaban cikin wata makala da ya rubuta wa jaridar Washington Post ta Amurka.

BBC ya ruwaito Buharin yana jaddada cewa shugabannin Turai sun sha nuna gazawa wajen cika alkawarin samar da dala biliyan 100 don shawo kan “matsalar sauyin yanayi da suka haifar da kansu” ga kasashe masu tasowa.

Ya kara da cewa daga yanzu ba zai yiwu kasashen Turai su rika tsara yadda ya kamata kasashen Afirka za su yi amfani da ma’adanan da suke da su ba.

“Kar ku fada wa ’yan Afirka yadda ya kamata su yi amfani da arzikinsu.

“ Da a ce Afirka za ta yi amfani da dukkan arzikin iskar gas da take da shi a rumbuna, wanda shi ne mafi inganci ga muhalli, hayaƙin da ke gurɓata yanayin duniya zai tashi daga kashi 3 cikin 100 zuwa 3.5.”

Afirka na fitar da kashi kusan uku ne kacal na hayaƙi mai gurɓata muhalli a duniya baki ɗaya amma tana cikin nahiyoyin da suka fi kowace fuskantar bala’in sauyin yanayin.