A shirye Najeriya take ta taimaka wa Turkiyya akan yaki da ta’addanci – Buhari

0
125

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya yi Allah-wadai da harin kunar bakin waken da aka kai birnin Istanbul na kasar Turkiyya a karshen mako.

Buhari ya ce Najeriya a shirye take ta tallafa wa Turkiyya wajen yaki da ta’addanci.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya fitar a ranar Lahadi.

Ya ce harin da aka kai ranar Lahadi kan wata gadar da mutane ke tafiya a kanta, wanda ya yi sanadin rasuwar mutane tare da jikkata wasu da dama abin kyama ne kuma aikin matsorata ne.

Buhari ya kuma ce, “Mutanen Najeriya sun bayyana rashin jin dadinsu da wannan harin.

“Muna ba Shugaban Turkiyya, Recep Tayyep Erdogan, tabbacin cewa gwamnati da al’ummar Najeriya za su ci gaba da tallafa musu a yakin da suke yi da ta’addanci.”

“Muna kuma yin addu’a ga iyalan wadanda harin ya ritsa da su, wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, sannan muna fatan samun sauki a kan lokaci ga wadanda suka sami raunuka,” inji Buhari.