Dan wasan Manchester United, Cristiano Ronaldo ya ce an yaudare shi a kungiyar, kuma baya ganin kimar Erik ten Hag, ana tilasta masa ya bar United.
An yi wa Ronaldo, mai shekara 37 alkawarin yana da rawar da zai taka a Old Trafford, bayan da bai samu barin kungiyar ba, wadda ta kasa samun gurbin Champions League kamar yadda ya yi fata.
Kyaftin din tawagar Portugal ya bayyana batutwa da dama a hirar da ya yi da Piers Morgan a shirin TalkTV.
An tuntubi United ko za ta ce wani abu kan zarge-zargen da Ronaldo ya yi.
Cikin batutuwan da Ronaldo ya bayyana a hirar da The Sun ta wallafa suna da yawa cikinsu:
- Wasu a kungiyar na tursasa masa sai ya bar kungiyar
- Babu wani gagarumin sauyi, tun bayan da Sir Alex ya yi ritaya a 2013
- Kungiyar ba ta damu da halin da ya shiga ba a lokacin da karamar yarinyarsa ta yi rashin lafiya a watan Yuli.
- Ban taba jin sunan tsohon koci, Ralf Rangnick ba, amma aka bashi aiki koci.
- Bai san dalilin da Wayne Rooney ya caccake shi ba, ”watakila ko don ya yi ritaya ni kuma har yanzu ina taka leada.”
Za a nuna hirar gabaki dayanta a gidan talabijin da yammacin Laraba da Alhamis.
Da aka tambayi Ronaldo ko mahukuntan kungiyar na son suga ya bar United, sai Ronaldo ya ce ”Haka ne, ba koci kadai ba har da wasu mutum biyu zuwa uku da suke da alaka da kungiya. An yaudare ni.