‘Yan bindiga sun bukaci kudin fansa miliyan 10 kafin sako gawar wanda suka sace a Kaduna

0
106

Wasu ‘yan bindiga a jihar Kaduna sun bukaci kudin fansa naira Miliyan 10 don bayar da gawar wani mai suna Obadiah Ibrahim da sukayi garkuwa dashi a makon da ya gabata.

Wani dan uwan marigayin mai suna Kefas Obadiah ne ya shaida wa manema labarai hakan a Kaduna, inda ya ce, tunda farko masu garkuwar sun karbi sama da naira miliyan uku daga gun ‘yan uwan marigayin, amma suka ki sako shi.

Kefas Obadiah ya ce, sun sace dan uwansa ne a cikin watan Oktoban 2022 a Sabon garin Gaya a yayin da yake kan hanyarsa ta dawo daga Abuja zuwa Kaduna.

Yayin tattaunawa da ‘yan bindigan, a farko sun bukaci kudin fansa naira miliyan 200 bayan cigaba da tattaunawa aka cimma matsaya akan biyan naira miliyan uku.

Kefas ya ce, masu garkuwar sun umarce mu da mu kawo masu kudin, bayan mun basu suka sheda mana cewa, za su yi amfani da kudin ne don sayen kayan abinci domin abincin su ya kare sai suka ce mana muje mu kawo masu naira miliyan 15.

Ya bayyana cewa, daga baya sun rage kudin fansar zuwa naira miliyan biyar suka kuma karbi babur daya, inda daga nan, bamu kara jin wani abu daga gurin su ba duk da kokarin da muka yi na yin magana da su ta waya, hakan ya ci tura.

Dan uwanmu ya mutu ne a ranar litinin, amma ba su sheda mana ba sai a ranar alhamis, inda ya ce, mun bukaci su bamu gawarsa amma sun ce sai mun biya kudin fansar gawar naira miliyan 10 Kafin su bamu gawar.