’Yan ta’adda 19 da sojoji ke nema ruwa a jallo

0
113

Rundunar Tsaron Najeriya ta sanya kyautar Naira miliyan biyar ga duk wanda ya ba da bayani da za su taimaka a kama ’yan ta’adda.

A safiyar Litinin rundunar ta fitar da jergin gawurtattun ’yan ta’adda 19 da suka addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, da kuma kyautar da ta sanya a kan kowannensu.

Sanarwar da Darektan Yada Labaran Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Jimmy Akpor, ya fitar ta ce yin hakan ya zama dole, domin ta ci gaba da ragargaza da kuma murkushe miyagun gaba daya, domin Najeriya ta samu kwanciyar hankali.

Ga jerin sunayen ’yan ta’addan:

  1. Sani Dangote: Dan asalin kauyen Dumbarum a Karamar Hukumar  Zurmi, Jihar Zamfara
  2. Bello Turji Gudda: Dan asalin kauyen Fakaia Jihar Zamfara
  3. Leko: Dan asalin kauyen Mozji, Karamar Hukumar  Matazu, Jihar Katsina
  4. Dogo Nahali: Dan asalin kauyen ’Yar Tsamiyar Ino, Karamar Hukumar Kankara, Jihar Katsina
  5. Halilu Sububu: Dan asalin kauyen Sububu, Karamar Hukumar Maradun, Jihar Zamfara
  6. Nagona: Dan asalin kauyen Unguwar Galadima, Karamar Hukumar Isa, Jihar Sakkwato
  7. Nasanda: Dan asalin kauyen Kwashabawa, Karamar Hukumar Zurmi, Jihar Zamfara
  8. Isiya Kwashen Garwa: Dan asalin kauyen Kamfanin Duadawa, Karamar Hukumar Faskari, Jihar Katsina.
  9. Alia Kachalla (Ali Kawaje): Dan asalin kuayen Kuyambana, Karamar Hukumar Dansadau, Jihar Zamfara
  10. Abu Radda: Dan asalin kauyen Zaranda, Karamar Hukumar Batsari, Jihar Katsina
  11. Dan-Da: Dan asalin asalin kauyen Zaranda, Karamar Hukumar Batsari, Jihar Katsina.
  12. Sani Gurgu: Dan asalin kauyen Zaranda, Karamar Hukumar Batsari, Jihar Katsina
  13. Umaru Dan Najeriya: Dan asalin kauyen Rafi a Karamar Hukumar Gusau, Jihar Zamfara.
  14. Nagala: Dan asalin Karamar Hukumar Maru, Jihar Zamfara.
  15. Alhaji Ado Aliero: Dan asalin kauyen Yankuzo, Karamar Hukumar Tsafe, Jihar Zamfara.
  16. Monore: Dan asalin kauyen Yantumaki, Jihar Katsina.
  17. Gwaska Dankarami: Dan asalin kauyen  Shamushele, Karamar Hukumar Zurmi, Jihar Zamfara.
  18. Baleri: Dan asalin Karamar Hukumar Shinkafi, Jihar Zamfara.
  19. Mamudu Tainange: Dan asalin kauyen Zaranda, Karamar Hukumar Batsari, Jihar Katsina.