Ebola ta kashe mutane 54 cikin kwanaki 55 a Uganda – WHO

0
132

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce cutar Ebola ta kashe mutane da yawansu ya kai 54 cikin kwanaki 55 da bullarta a Uganda, dai dai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar masu harbuwa da cutar.

Cikin rahoton da WHO ta fitar kan yadda cutar ta Ebola ke ci gaba da lakume rayuka a Uganda, ta ce yankin Mubende da ke tattara alkaluman na da mutane 29 cikin mutanen 54 da cutar ta kashe.A cewar rahoton daga lokacin da cutar ta bulla a ranar 20 ga watan Satumba zuwa yanzu an samu mutane 137 da aka tabbatar sun kamu da ita yayinda wasu 65 kuma suka warke.

Hukumar ta WHO ta ce yankunan da cutar ta fi yaduwa a sassan Uganda sun kunshi Kassanda da Kyegegwa da kuma Kagadi baya ga Bunyangabu da Wakiso da kuma Masaka da Kampala.

WHO ta ce yankunan Mubende da Kassanda inda ta fi tsananta na jumullar mutum 63 da kuma 47 da zuwa yanzu ke jinyar cutar ta Ebola.

Dukkanin yankunan dai yanzu haka na karkashin killacewar kwanaki 21 a kokarin dakile yaduwar cutar, wanda ya sa tun daga ranar 10 ga watan nan ba a sake samun wanda ya harbu ba.