An kashe shugabannin ’yan ta’adda Halilu Sububu da Gwaska Dankarami

0
109
Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasara kashe wasu kasurguman ’yan ta’adda biyu  Halilu Sububu da Gwaska Dankarami  da mayakansu a wannan Talatar.

Nasarar da rundunar ta samu na zuwa ne bayan kwana guda da bayyana sunayen ’yan ta’adda a cikin jerin kwamandojin masu tayar da kayar baya 19 da take nema ruwa a jallo.

A ranar Litinin da ta gabata ce Babban Ofishin Tsaro ya fitar da sunayen kwamandojin ’yan ta’addar guda 19 da suka fitini duk yankunan Arewa, tare da sanya tukwicin naira miliyan biyar kan kowane daya daga cikinsu ga duk wanda ya bayar da muhimman bayanan da za su kai ga cafke su.

Jerin sunayen ’yan bindigar da Babban Ofishin Tsaron ya fitar ta bakin Daraktan Sashen Yada Labarai, Manjo-Janar Jimmy Akpor, sun hada da: Sani Dangote da Bello Turji Gudda da Leko da Dogo Nahali da Halilu Sububu da Nagona da Nasanda da Isiya Kwashen Garwa da Ali Kachalla (Ali Kawaje) da kuma Abu Radde.

Sauran su ne; Dan-da da Sani Gurgu da Umaru Dan Najeriya da Nagala da Alhaji Ado Aliero da Monore da Gwaska Dankarami da Baleri, sai kuma Mamudu Tainange.

Sai dai wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa, rundunar Operation Hadarin Daji a ranar Talata ta kawar da biyu daga cikinsu daga doron kasa, a yayin da take ci gaba da yi wa sansanoninsu barin wuta ba dare ba rana.

Daya daga cikin majiyar ta bayyana cewa, sojojin sun yi luguden wuta ta sama da kasa kan maboyar Alhaji Ganai da ke Dajin Kidandan a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Majiyar ta ce daga bayanan da suka samu an kashe Halilu Sububu da Gwaska Dankarami da kuma da dama daga cikin mayakansu.

A cewarta, mayakan nasu da aka kashe sun hada da; Ceri, Dan Musulmi, Danbarkeji, Guguwa, Dan Sha Bakwai, Marshall da kuma Hana Zuwa.

“Sakamakon hare-haren da aka kai wa gidan Alhaji Ganai, an kashe ’yan ta’adda da dama ciki har da Yellow Kano, wani na hannun daman jagoran ’yan ta’addan da kuma karin wasu masu tayar da kayar baya bakwai,” a cewar daga cikin majiyoyin.

Sai dai kokarin da wakilinmu ya yi na neman jin ta bakin daya daga cikin kakakin rundunar sojin sama da na kasa, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.