Yayin da ya rage kwana 100 daidai kafin babban zaben 2023, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gargadi jam’iyyun siyasa da ‘yan takaransu da su tafiyar da harkokinsun cikin lumana, kana su guji tayar da kayar baya da haddasa rarrabuwan kan jama’a.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya yi wannan gargadi cikin sakonsa mai taken “100 Kafin Babban Zaben 2023″ da ya fitar ranar Laraba a Abuja.
A ranar 25 ga Fabrairu, 2023 ce za a fara gudanar da zabe inda ake sa ran farawa da na Shugaban Kasa da na ‘yan Majalisar Tarayya.
Kamfnin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ce, Yakubu ya jaddada kudirin hukumar na yin amfani da na’urar BVAS wajen tantance masu kada kuri’a da aikewa da sakamako yayin zaben.
Ya kara da cewa, yin amfani da fasahar zamani zai taimaka matuka wajen gudanar da sahihin zabe kuma mai tsafta.
Daga nan, Yakubu ya yi kira ga ‘yan kasa da su shiga harkokin zabe a yi da su, musamman shirin fitar da sunayen masu zaben da aka yi wa rijista da ke gudana.
Ya ce, sanin ‘yan Najeriya ne cewa, sha’anin zabe abu ne mai bukatar hannu da yawa, don haka ya ce za su ci gaba da gudanar da harkokinsu yadda ya kamata kuma daidai da tanadin doka.
“Muna rokon masu ruwa da tsaki da daukacin ‘yan kasa, kowa ya yi aikin da ya rataya a kansa don mu yi aiki tare wajen gudanar da irin zaben da ‘yan Najeriya ke buri.
“Yau saura kwana 100 daidai kafin bude rumfunan zabe a ranar 25 ga Fabrairu don gudanar da manyan zabubbuka (na Shugaban Kasa da ‘yan Majalisar Tarayya),” in ji Yakubu.