Shugaba Buhari ya amince da yi wa ma’aikatan shari’a ƙarin albashi

0
88

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da shirin ƙara wa ma’aikatan shari’a albashi.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yau Juma’a a jihar Rivers, lokacin ƙaddamar da sabon ginin makarantar horas da lauyoyi da ke jihar.

Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami, wanda shi ne ya wakilci shugaban ƙasar, ya ce gwamnatin ƙasar tana ƙoƙarin inganta albashin ma’aikatan shari’ar ne domin ƙarfafa ɓangaren da kuma tabbatar da ƴancinsa.

Ya ce yanzu haka shugaba Buhari ya umurci shugaban hukumar tarawa da raba kuɗaɗen haraji na ƙasar, da ministan sharia’a su ɗauki matakan ganin an fara aiwatar da ƙarin albashin.