Wani soja ya bude wuta a wani sansanin sojoji da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya inda ya kashe soja guda da wani ma’aikacin agaji tare da raunata wani matukin jirgin sama mai saukar ungulu na Majalisar Dinkin Duniya.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa tana mai cewa sojojinta da ke wurin sun yi nasarar kashe sojan da ya kai harin a jihar ta Borno.
Ta kuma bayyana shi a matsayin ‘bijirarren soja’.
Rundunar sojin Najeriyar ta kuma ce : An wuce da matukin jirgin da aka raunata zuwa asibiti kuma yana samun kulawar da ta kamata.
Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin da ya sa sojan ya kai wannan harin ba.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da rana.
Rundunar sojin Najeriyar ta ce an fara gudanar da cikakken bincike a kan ”abin takaicin da ya faru.”
Dubban sojojin Najeriya na ci gaba da gwabza fada da kungiyar Boko Haram da kuma reshenta da ake kira ISWAP a arewa maso gabashin kasar a cikin shekaru sama da 10.
Kungiyoyin agaji na cikin gida da na kasa da kasa na tallafa wa miliyoyin mutane da rikicin ya daidaita wanda kuma ya yi sanadin mutuwar mutum kusan dubu 350 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.