Hukumar Bada Lamuni ta Duniya IMF ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta kaddamar da bincike akan man fetur din da kamfanin NNPC ya ce ana sha a cikin kasar da kuma irin kudaden tallafin da ake zubawa da sunan talaka.
Hukumar ta ce abin takaici ne yadda kamfanin ke tafka asara sakamakon kashe makudan kudade da biyan dimbin basussuka, yayin da ake hasashen karuwar basussukan nan gaba kadan, abin da ke yi wa kasar illa wajen samun damar karkata kudaden da take samu wajen ayyuka na musamman a bangaren ilimi da kula da lafiyar jama’a.
IMF ta ce duk da karuwar kudaden shigar da gwamnati ta samu a shekarar 2021 wadanda ba su da nasaba da man fetur, Najeriya ta samu gibin kasafin kudin da ya kai sama da kashi 6 a wannan shekara saboda irin makudan kudaden da ake zubawa da sunan tallafin man fetur.
Hukumar ta ce muddin gwamnati ba ta sake fasalin inganta kudaden harajinta ba, tallafin man da kudaden ruwan da take biya akan bashin da ta ciwo na iya zarce kashi 6 na gibin kasafin kudin kasar nan da shekarar 2027.
IMF ta bukaci karfafa ayyukan noma da samar da abinci a Najeriya, yayin da take cewa nan da shekaru 10 masu zuwa za a bukaci sabbin masu bukatar ayyukan yi miliyan 25.
Yayin da take jaddada matsayinta na ganin Najeriya ta cire tallafin mai gaba daya, hukumar ta kuma bukaci gwamnati da ta tashi tsaye wajen yaki da barayin man fetur wadanda ke neman durkusar da kasar.