Buhari ya taya Jonathan murnar cika shekaru 65

0
110

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya taya tsohon shugaban kasa Dakta Goodluck Ebele Jonathan murnar cika shekaru 65 a duniya, a madadin gwamnati da ‘yan Nijeriya.

Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar, ya bayyana matsayinsa na musamman da tsohon shugaban kasar yake da shi wajen ci gaban kasa, tare da sadaukarwa da kuma samun nasarar sace zukatan ‘yan Nijeriya da kuma al’ummar kasar nan a matsayinsa na mai zaman lafiya, ta hanyar ci gaban kasa da samar da sulhu da kishin kasa a kasashe da dama.

Shugaban ya bi sahun ‘yan uwa, musamman matarsa, Patience da mahaifiyarsa Eunice, wajen murnar wani gagarumin ci gaba a rayuwar tsohon shugaban, inda ya tuna tafiyarsa ta siyasa, wadda a bayyane ta ke ya kasance mai kishin kasa wanda ya fara a matsayin mataimaki.

Ya yi Gwamna daga 1999 zuwa 2005, ya saje yin Gwamna daga 2005 zuwa 2007, sai mataimakin shugaban kasa, dava 2007 zuwa 2010 da kuma shugaban kasa, daga 2010 zuwa 2015.

Shugaban ya yi imani da zumunci, aminci, da tawali’u na Dakta Jonathan na ci gaba da bude damar yin hidima ga bil’adama tare da bayyana hanyar da tsohon shugaban kasar zai iya saka hannun jari a cikin mutane, cibiyoyi, da kasashe.