Gine-gine a kan layin wuta ne ya hana inganta lantarki a Kano – Minista

0
117

Ministan Lantarki na Najeriya, Injiniya Abubakar D. Aliyu, ya ce gine-gine da mutane ke yi a kan hanyar layin wutar lantarki a jihar Kano na kawo cikas ga aikin inganta wutar.

Ministan ya bayyana haka ne a yayin ziyarar aikin da ya kai tashoshin rarraba wutar lantarki da gwamnati ta gina a Kumbotso da Rimin Zakara da ke Kano.

Injiniya Abubakar ya ce, gwamnati tana son kara yawan karfin wutar lantarki da Kano take samu zuwa megawatt 2,000, amma an kasa yin hakan saboda mutane sun gina gidaje a kan hanyar da babban layin wutar ya bi.

Yayin ziyarar, Ministan ya zagaya tashar lantarki ta Dan Agundi tare da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, inda ya roki Gwamnan da ya sa baki domin ganin cewar an kawar da gidajen da suka yi kutse a kan layin lantarki daga Kumbotso zuwa Dan Agundi.

Ministan lantarkin ya kuma ce babbar tashar lantarki da ke Rimin Zakara za ta bayar da damar kara yawan wutar lantarki da ake samu a jihar Katsina.

Sannan ya ce Gwamnatin Tarayya karkashin Shugaba Muhammadu Buhari ta dukufa wajen mayar da Kano wata babbar cibiya ta rarraba wutar lantarki a Arewacin Najeriya.

Dangane da haka, ya ce Gwamnatin na gudanar da wani shiri tare da hadin gwiwar kamfanin Siemens na Jamus domin ingantawa da kuma kara yawan wutar lantarki da ’yan Najeriya suke samu a yanzu.