Mutum 10 sun mutu bayan da motarsu ta faɗa cikin dam a Kano

0
126

Hukumomi a jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum goma sakamakon mummunan hadarin mota.

Lamarin ya auku ne ranar Asabar lokacin da wata mota dauke da fasinjoji ta faɗa madatsar ruwa cikin ƙaramar hukumar Gwarzo.

Saminu Yusuf Abdullahi shi ne jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe Gobara ta jihar Kano ya shaida wa BBC cewa wata motar Golf ɗauke da fasinjoji ce ta ƙwace sakamakon fashewar taya ta faɗa cikin madatsar ruwa ta Fade Dam.

Ya ƙara da cewa ”da taimakon Allah da taimakon jami’an hukumarmu da kuma masinta mun samu nasasar tseratar da mutum uku a raye”

Jami’in ya kuma ce mutum goma ne suka mutu sakamakon aukuwar lamarin.

Ya ci gaba da cewa fasinjojin na kan hanyarsu ta zuwa Katsina daga jihar Kano.